Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

 

Shugaban Amurka Donald Trump ya yabawa jami’an tsaron da ke gadin fadarsa ta White House saboda bindige wani mahari da ya bude wuta a wajen fadar, abin da ya sa a ka ruga da shi.

An ga lokacin da wani jami’i da ke tsaron lafiyar shugaban ya tunkari inda yake cikin hanzari yayin da yake tsaka da amsa tambayoyin manema labarai tare da yin waje da shi.

”Ranka ya dade dole mu bar wajennan kawai ” in ji jami’in da ya tunkari shugaba Trump yana magana gare shi kai tsaye, yayin da shugaban ke gabatar da jawabin da ya saba yi kan cutar korona a kullum.

Yan mintuna daga baya ne shugaba Trump ya sake dawowa, tare da bayyana cewa jami’an tsaro sun harbi dan bindigar da ya kai harin, don haka an tafi da shi asibiti.

Lamarin dai ya janyo killace fadar ta White House har tsawon awanni.

Bisa doka jami’an tsaron fadar mulkin Amurka ta White House kan killace fadar tare da hana zirga-zirga duk lokacin da a ka fuskanci akwai wata barazana ta tsaro, da ka iya cutar da zababbun muhimman mutane biyu da fadar ke dauke da su wato shugaban kasa da mataimakinsa, da kuma iyalansu.

Ba wannan ne karon farko da aka killace fadar ba, don ko a kwanan baya lokacin da zanga-zangar kyamar kisan George Floys ta tsananta a birnin Washington DC jami’an tsaro sun killace ta, tare da umartar shugaban ya shiga gidan karkashin kasa.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *