Daga-Nura Aliyu

Gwamnatin Jahar Kano ta ce dokar nan data haramta yin goyo a mashin Mai kafa biyu tana nan daram, Kuma za a kama duk kan wanda ya karyata.
Jami’an Hukumar Karota zasu cigaba da Kama duk mutumin da yayi goyo daga ranar Alhamis din nan.
Shugaban Hukumar KAROTA ta Jahar Kano Baffa Babba Dan’agundi, ya bayyana haka lokacin taron manema labarai daya gudanar a ofishinsa da yammacin ranar laraba.
Shugaban Hukumar Karotar yace Jami’an hukumar zasu fara kama duk kan Mai abin hawan da bai sanya kyallen rufe hanciba..
Wakilinmu Nura Aliyu, ya rawaito mana cewar hukumar tace ta Kori wasu ma’aikatanta su biyar daga bakin aiki, saboda samunsu da aikata laifufuka iri daban daban.
Sannan ta jaddada cewa zataci gaba da daukar tsauraran matakai akan duk kanin wani Jami’in ta daya aikata abinda bai.
Shugaban Hukumar KAROTAn ya kuma shawarci jama’a dasu kai korafinsu ga hukumar idan wani Jami’i yaci zarafinsu.