Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Jaridar Daily Nigeria ta rawaito Dangote, BUA, Tiamin Rice sun sanar da niyyarsu ta ɗaukar ɗalibai 370 da suka ci gajiyar tallafin karatu na ƙasar waje wanda tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya ba su.

An yi wannan sanarwa ne a ranar Asabar lokacin da ake taron ƙaddamar da samar da aikin yi ga ɗaliban ƙasar waje da Kwankwaso ya ba wa tallafi.

Mansur Ahmad na kanfanin Dangote da Idi Hong na kanfanin BUA and Sagir Ahmed na kanfanin Tiamin Rice sun tabbatar da cewa kowannensu zai ɗebi kasonsa domin ba su ayyuka.

Sun tabbatar da cewa ɗaliban waɗanda mafi yawa ke digiri mai daraja ta ɗaya (first class) za su dace da kanfanunuwansu.

A lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa, Kwankwaso ya ce ya yi farin cikin ganin ɗaliban da gidauniyarsa ta ɗau nauyi sun dawo cikin ƙoshin lafiya da kuma digirinsu na biyu a ɓangarori daban-daban.

Ya ƙara da cewa ɗaliban dai sun ci gajiya tallafi ne da ya haɗa da biya musu kuɗin makaranta, kuɗin jirgi, wurin kwana da na rayuwa ta yau da kullum a yayin da karatun nasu.

Sannan gwamnan ya bayyana cewa jami’ar ta Mewer dake Indiya ta ba wa mutane sha uku cikin ɗari uku da saba’in aikin lakcarin tare da tallafin karatun digiri na uku (PhD).

Ɗaliban dai akwai na Indiya da Sudan da Dubai, duk ƙarƙashin gidauniyar ta Kwankwasiyya.

Wasu daga cikin iyayen yaran sun yaba wa Kwankwaso kan wannan aikin alheri tare da jan hankalin ɗaiɗikun mutanen kan su yi koyi da shi.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *