Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Daga -Abubakar Sale Yakub

Ginin Asibiti da Tanki da Chemist da Mabuga da Daneji Amintacciya ta samar a unguwar

Kungiyar Daneji Amintacciya ta kafu shekaru 20th, da suka gabata, cikin wadannan shekaru kungiyar ta gudanar da ayyukan cigaba a yankin unguwar Daneji masu tarin yawa.

A akwai wani gagarumin aiki da jagororin kungiyar Daneji Amintattciya suka wuce gaba wajen samo shi na sanya sabuwar wayar lantarki dan warware matsalar haduwar da waya take a lokacin baya, hakan yasa wutar lantarkin unguwar ta inganta domin babu wata matsala a yanzu ta wannan fuska.

A bangaren abin daya shafi lafiya kuwa; Kungiyar Daneji Amintacciya ta samar da karamin Asibiti da Chemist wanda yake da magunguna akan farashi mai sauki dan tallafawa al’ummar unguwar.

Duba da yadda Duniya ta sauya ta fuskar harkokin sadarwa hakan yasa wannan kungiya ta Daneji Amintacciya ta samar da cibiyar horas da matasa yadda zasu sarrafa na’urar Computer.

Ta fuskar dogaro da kai Kungiyar ta samar da mabuga wadda dimbin matasan unguwar suke samun abin da zasu rike kansu har da iyayensu.

Wannan kadan ne daga cikin ayyukan cigaba da Kungiyar Daneji Amintacciya ta samar kar kashin Malam Salisu Mai manja da Malam Ahamd Abba da Malam Ghali Ishaq da dai sauran shugabanni baki daya.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *