Farashin tikitin jirgin sama ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya. Kamfanonin jiragen sama a kasar sun ce tashin farashin tikitin jiragen na da alaƙa da abubuwa da dama da suka hada da tashin da dalar Amurka ta yi a kan kudin Naira na Najeriya da kuma annobar cutar korona.
Kaftin Ado Sanusi shi ne shugaban kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Aero Contractors a Najeriya wanda ya shaida wa BBC cewa yawan jiragen da ke tafiye-tafiye a sararin samaniyar Najeriyar sun ragu, yayin da kuma yawan mutane masu yin tafiye-tafiye ya ƙaru, don haka sai wadanda suke da kudi da yawa su za su fi iya sayen tikiti.
”Jiragen da suke kasar waje na kamfanoni ba a iya dawo da su da wuri ba, kana mu da muke gyaran jirage a nan kasar ya zamar mana akwai wahala mu samu kayayyakin gyara saboda duka Turai a kulle take – ka ga ba za su iya aiko mana kayayyakin gyara su ci gaba da zirga-zirga ba,” in ji Kaftin Sanusi.
Ya kuma kara da cewa babu wani kamfanin zirga-zirgar jiragen sama da yanzu ko shekara daya da ta wuce da suka sake sayen sabbin jirage suka saka cikin zirga-zirgar, don haka shi yasa duk jiragen da suka lalace sai dai a ajiye
Ko shakka babu hakan zai iya sakawa ko nan gaba farashin tikitin jiragen saman ba zai sake dawowa a zuwa farashinsa na da ba,” in ji shi.
A baya-bayan nan a Najeriya hauhawar farashin tikitin jirgin sama da kuma rashin tabbas sun jefa fasinjoji cikin halin damuwa da ƙaƙa-ni-ka-yi.
Satar mutane don kuɗin fansa, na cikin dalilan da suka sa ɗumbin mutane gwammace hawa jirgin sama duk da tsadar tikitinsa.
Sai dai, ga alama duk da tsadar, a yanzu a iya cewa hawa jirgin sama ya fara zama, wani babban jidali.
Karuwar farashin tikitin jirgin saman na ci gaba da haifar da ce-ce-ku-ce a kasar musamman a tsakanin fasijoji, inda suke kokawa da tsadar tikitin.
Samun tikitin dai ya zama wani jidali ko da kuwa da kuɗinka kasancewar akwai mabuƙata da yawa, wani lamari da ba a saba gani ba, kamar yadda fasinjoji da dama suka shaida wa takaicinsu game da karuwar farashin tikitin.
“Sai da na biya fiye da naira 500,000 zuwa jihata ta Gombe don hutun ƙarshen shekara daga Legas ni da matata da yarana uku kawai. Wannan wane irin tashin hankali ne?” kmar yadda wani fasinja ya koka.
Kamfanonin jiragen sama a kasar sun ce lamarin yana da alaƙa da abubuwa ciki har tsadar dala da kuma kasancewar shekara ta zo karshe, baya ga matsalar tsaro.
Wasu bayanai na cewa wannan lamari na tsadar farashin tikitin jirgin sama a Najeriya zai ci gaba da kasancewa har zuwa cikin tsakiyar shekara mai zuwa, kuma akwai yiwuwar farashin zai ci gaba da ƙaruwa kaɗan-kaɗan har zuwa lokacin da kamfanoni jiragen sama za su kammala gyaran jiragensu