Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce dangane da matakin da gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ɗauka na dakatar da Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu daga kan muƙaminsa.
Shi dai Wazirin Zazzau ya kasance ɗaya daga cikin mutum biyar da ke zaɓen Sarki a masarautar, kuma an dakatar da shi ne a dai-dai lokacin da ake ci gaba da ƙalubantar nadin Ambasada Ahmadu Bamalli a gaban kotu, a matsayin sabon Sarkin Zazzau na 19.
Tun a makon jiya ne ake ta yayata sanarwar dakatar da Wazirin Zazzau ɗin Alhaji Ibrahim Aminu a shafukan sada zumunta, inda aka ambato babban sakatare a ma’aikatar ƙananan hukumomi da masarautu ta jihar Kaduna, Musa Adamu a matsayin wanda ya sanya hannu a takardar dakatarwar a madadin kwamishina mai kula da ma’aikatar Jafaru Sani.
Wannan mataki ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin jama’a a tare da zazzafar muhawara kan dalilan da suka sa aka dakatar da basaraken.
Yayin da wasu ke danganta matakin a kan rashin halartar Wazirin wani taro da ma’aikatar kula ƙananan hukumomi da masarautu ta gayyace shi, wasu kuwa cewa suke an dakatar da shi ne saboda ya ƙi amincewa ya sauya matsaya kan wanda gwamnan jihar ke son ya zama Sarki.
Abin da ya faru a lokacin da masu zaɓen Sarki wanda Wazirin na Zazzau ya jagoranta suka miƙa sunayen mutum uku waɗanda kuma cikin su, babu wanda gwamnan jihar ke so.
Wani ƙaulin kuma na cewa, ƙin amincewar Wazirin na Zazzau na sauya lauyan da ke kare shi a sharia’ar da ake yi kan naɗin Sabon Sarkin wanda shi kansa Wazirin tare da sauran masu zaɓen Sarki ke cikin waɗanda ake ƙararsu.
A ɓangare guda kuma wasu rahotanni na cewa, an dakatar da Wazirin na Zazzau ne saboda zargin sa a kan kwarmata wa ‘yan jaridu takardar da masu zaben Sarkin suka gabatar wa gwamnatin jihar na wadanda suka zaba domin ya gaji Marigayi Dr Shehu Idris.
Yunkiri jin ta bakin wazirin yaci tura,