Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Dalibai tare da malaman kwalejin kimiyya ta Kagara da ke jihar Neja sun isa babban birnin jihar, Minna.

Dalibai 27, malamai 3 tare da wasu mutum 12 ne aka sace yayin harin da aka kai makarantar.

A wani bidiyo, an ga daliban suna fitowa daga dajin. An gano cewa an nadi bidiyon a wurin makarantar sakandare na Attahiru da ke Madaka a jihar Neja.

– Dalibai da malaman kwalejin kimiyya ta Kagara sun isa garin Minna ta jihar Neja

– A safiyar yau ne aka tabbatar da sako daliban daga hannun ‘yan bindigan da suka sace su

– Kwamishinan ilimi na jihar ne zai fara karbarsu kafin su samu ganawa da gwamnan

Dalibai tare da malaman kwalejin kimiyya ta Kagara da ke jihar Neja sun isa babban birnin jihar, Minna.

Dalibai 27, malamai 3 tare da wasu mutum 12 ne aka sace yayin harin da aka kai makarantar.

A wani bidiyo, an ga daliban suna fitowa daga dajin. An gano cewa an nadi bidiyon a wurin makarantar sakandare na Attahiru da ke Madaka a jihar Neja.

KU KARANTA: Sabon tashin hankali: ‘Yan bindiga sun sheke mutum 22 a wurin hakar gwal a Zamfara

Jibrin Usman, kakakin ma’aikatar ilimi ta jihar Neja ya ce an tuntubi kwamishinan ilimi na jihar domin ya karba yaran kafin su gana da gwamnan jihar.

Daya daga cikin iyayen daliban ya sanar da Daily Trust cewa an sako su kusa da Madaka a karamar hukuma Rafi ta Neja.

Mahaifin dalibin ya ce zai cire dan shi daga makarantar da gaggawa, inda ya kwatanta da hakan da abinda duk wani uba nagari zai yi.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *