Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

By Abdullahi Isah

Yaki na cigaba da rinchabewa tsakanin dakarun sojin Turkiyya dana Syria kan yankin Idlib dake zaman wuri daya tilo daya rage a hannun ‘yan tawayen Syria.

An bayarda rahotannin dake cewa sojojin Turkiyya Sun harbo jiragen yakin Syria guda 2 lokacin da suke maida martani ga dakarun Syria da suka kakkabo jirgin Turkiyya mara matuki.

Ministan tsaron Turkiyya Hulusi Akar, yace harin ramuwar gayya da Turkiyya ta kaddamar, yayi sanadiyyar lalata tankokin yakin Syria da dama tareda na’urorin kakkabo makamai.
Fararen hular yankin na cigaba da shiga tsaka mai wuya sakamakon luguden wuta babu kakkautawa da sojojin gwamnati keyi.

A hannu guda kuma, Kasashen Tarayyar Turai sun datse iyakokinsu domin hana ‘yan gudun hijirar kwarara cikin kasashensu.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *