Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamnatin Najeriya ta ce sai nan da shekarar 2025 za a kammala aikin hanyar Abuja zuwa Kano da aka fara a 2018.

Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki a Kaduna, na wani babban ayari na gwamnatin tarayya.

“Nan da shekarar 2022 ne za a kammala hanyar da ke tsakanin Kaduna da Zaria, wanda wannan babban ci gaba ne.

“A 2023 za a kammala hanayar da ta tashi daga Kaduna ta dangane ga Kano, sai kuma a 2025 za a kammala hanyar Abuja zuwa Kano baki ɗayanta,” in ji Fashola.

Tawagar gwamnatin tarayyar ta ziyarci aikin da ake yi tsakanin Kaduna zuwa Kano inda ta ce ta gamsu da yadda ake gudanar da aikin, duk kuwa da cewa wasu al’ummar ƙasar na ƙorafi kan yadda wannan aiki ke tafiyar hawainiya.

Cikin tawagar har da shugaban ma’aikatan shugaban kasa Ibrahim Gambari, wanda ya wakilci Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce “mun gamsu da ingancin aikin a wuraren da aka kammala, duk da cewa akwai ‘yan matsaloli.”

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, na cikin tawagar sai dai ra’ayinsa ya sha bamban da na ministan ayyukan, in da ya ce ” za’a kammala aikin cikin wannan lokaci da shugaba Buhari ke jagorantar Najeriya.”

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *