- A yayin da aka shiga rana ta biyu da fara tantance yan wasa kwallon kafa a jihar Kano Shugaban kungiyar ATM Sport Academy Jamyl MD Abubakar yace atisayen da kungiyar sa ta shiryawa matasan yan wasa a jihar kano ta haska irin dinbin matasan dake da basirar kwallon kafa a yankin arewacin najeriya,
Jamyl wanda ya shafe kwanaki uku yana halartar filin tantance yan wasa a garin Dawakin Kudu yace daga abin Daya gani daga yan wasan akwai tabbacin cewa yankin arewacin kasar nan nada managartan yan wasa da zasu zama abin alfahari ga yankin nan bada jimawa ba,
Jamyl MD wanda ya yaba da yadda zaben yan wasan ke gudana ba tare da son rai ba, yace hakan wata yar manuniyace da take nuna irin adalcin da masu zaben keyi wajen gudanar da amanar da aka danka musu,
Da yake martani kan yadda wasu ke kokawa kan rashin samun damar shiga shirin Jamyl MD cewa yayi kwallon kafa nada kaidoji na fara ta da suka hadar da zuwa fili akan lokacin da aka tsara ba tare da makara ba, saboda haka duk lokacin da muka sanya zamu fara training to bamason makara don ta hakane muke gane irin yadda dan wasan zai zama inya samu shiga saboda haka kiyaye kaidojin mu na daga cikin abinda muke dubawa,
Akan ko arewacin najeriya nada yan wasan da zasu iya gogayya da takwarorisu na kudanci MD Jamyl cewa yayi kwarai akwai kuma yan wasan arewa ma nada abubuwan dana kudancin kasar basu dasu kamar Hakuri, juriya, alkawari da yakana abubuwan da Jamyl din ke cewa suna daga daraja da martabar yan wasa,
Da yake Karin haske kan yadda kungiyarsa ke son ganin yan wasan kwallon kafa ayankin arewa sun kasance Jamyl cewa yayi shiya yasa muke bijiro da irin wadannan managartan shirya shiryen dan muga wadanda ke bukatar taimako da inda zamu taimaka musu,