Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Ruwan sha, Hanyoyi, Wutar Lantarki, Samar da Ayyuka da Samar Sanaoin dogaro kai na daga cikin alkawuran da yan siyasa kan yi lokacin da suke neman a zabesu,

Ga wakilin karamar humumar Bichi a Majalisar Wakilai Takasa Honarable Injiniya Abubakar Kabir Abubakar Bichi, Ace kwalliya ta fara biyan Kudin sabulu duba da yadda yake gudanar da ayyukan Raya Kasa daki daki na a gani a taba wanda ke taba rayuwar alumma kai tsaye,

Samar ruwan sha, dayane daga cikin abin da Injiniya ya sanya a gaba saboda yadda wasu alumomin yanki ke matukar bukatar sa Rauwan Shan na daga cikin abin da garin Tinki, Fagwalo,da Kau Kau a Danfako suke  ke bukata shekaru da dama amma basu samu ba sai a wannan lokaci da Injiniya Abba ya kawo musu famfo mai amfani da hasken Rana wato SOLAR a turance, inda aka fidda kai  goma sha biyar a kowane gari dan amfanin alummar garuruwan tinki mazabar Kwamarawa, Fagwalo da Kaukau ga alummar garuruwan  Kwalliya Tabiya Kudin Sabulu murna sai kace ranar sallah manya da yara mata da maza kowa murna Abba ya kawo karshen rashin ruwa, ko dogon zango kafin a samu ruwa,a garin Tinki,

Irin wannan hali gari fagwalo da Dan fako a garin Kau Kau ya kasance inda suma suka amfana da irin wancan aikin samar da ruwan sha, a sakonsa ga alummar garuruwan Dan majaliasar ya bukaci alummar da sukaci moriyar wannan aiki dasu sanya ido dan kare wandannan kayayyaki daga bata gari, tare da alkawarin cigaba da samar da ayyuka da zasu bunkasa cigaban alummomin Bichi da kewaye,

Sashin kafar sadarwa ta Express Radio zai cigaba da bibiyar irin wadannan ayyukan more rayuwa da wakilin Bichi a Majalisar wakilai ta kasa ke kawo wa Alummarsa,

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *