Duk da samun nasara a wasanni 2 a jere da kungiyar kwallon kafa ta Giodano fc tayi a gasar wasan kwallon kafa ajin matasa ta kakar 2020-2021 da aka fara a makonnan maihorar da kugiyar kwallon kafa ta Giodano fc dake fafata wasa a shiyyar Jos Abubakar Zagalo yace har yanzu da sauran tafiya,
A tattaunawarsa da expressradiofm.com coach Zagalo cewa yayi akwai sauran aiki a gaba duba da cewa wasannin gaba da zaa buga zasuyi zafi fiyeda na farko saboda wasane na yada kanin wani, kuma a lokacin da wasu ke Neman zama kan gaba wasu tsira suke nema kuma babu shakka zamu hadu da irinsu.
Da yake bayani kan nasarori biyu da kungiyarsa ta samu a gasar Coach Zagalo cewa yayi nayi murna matuka saboda kalubalen yafi a kanmu saboda duk kungiyoyin sun san Giodano kungiyace datazo daga ajin Kwararru dan haka babu wanda zai riketa da saujki,
Kan yadda yan wasan ke taka rawar gani coach zagalo cewa yayi ba abin mamaki bane saboda irin goyon baya da mai kungiyar ke bawa yan wasan damu masu horarwa abin ya sa kowa na kokarin sai ya saka masa da irin abinda yakeyi,kuma sauran masu ruwa da tsaki na kungiyar na bamu cikakken goyon baya hakan mana jin dadi kwarai,
Zagalo yace wani abin jindadi shine yadda shugaban kungiyar Jamilu Wada Aliyu ya aminta da yadda muke gudanar da aikinmu ba sa baki illa karin karfin gyiwa da kullum yake yi mana to ya taimaka mana samun nutsuwa a shirye shiryen mu inda yace ” Giodano ba irin sauran kungiyoyi bace, wannan kungiyar akwai tsari inda kowa ke aikinsa kanar yadda aka tsara
Da yake amsa tambayar ko ya yake kallon makomar kungiyar a karshe gasar Zagalo cewa yayi ” ai ba kallo ko kare matsayi mukazo ba, munzo neman abin dayake namune wato tikitin PRO league wanda kafi kowa sanin daga inda mukazo nan,fatan kawai Allah ya tabbatar mana da kayan mu ” inji zagalo
Kungiyar Giodano na daya daga cikin kungiyoyi da suka dawo wasan ajin matasa rukuni na daya daga wasan kwararru bayan shafe shekaru biyu a gasar inda kungiyar ke fatan komawa, shugaban kungiyar Jamilu Wada Aliyu ne ke daukar nauyin kungiyar batare da tallafin gwamnatiba tsawon shekaru 10 kuma na daya daga cikin kungiyoyi kalilan da suka dade a gasar kwararru kafi faduwarsu a shekara ta 2019