Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Mataimakin na musamman ga kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kano kuma wakilin kwamishina a kwamitin tsara gasar wasan kwallon kafa tsakanin kananan hukumomin jihar Kano Kabiru Abdullahi Garo yace sabuwar gasar wasan kwallon kafa tsakanin kananan hukumomin jihar kano da maaikatar kananan hukumomi ta shirya a karon farko bayan kimanin shekaru 5 ba tare da anyi gasar ba wata alamace da take nuna irin hangen nesa da kwamishinan kananan hukumomin jihar Hon Murtala Sule Garo ke dashi na dawo da wasannin dake haska irin matasa masu basira da kananan hukumomi ke dasu,

A hirarsu da wakilin express radio online Kabiru Garo cewa tuni maaikatar kananan hukumomi ta sahalewa kowace karamar hukuma ta shirya dan tunkarar gasar da kungiyoyi 8 zasu fafata a karshen mako a filin wasa na garin dawakin kudu a wasan share fage da zai alamta fara gasar da zaa buga wasanni 4 da yake karin haske kan wasannin kananan hukumomi kamar na Kofin Gwamna (Governor Cup tag Ganduje Cup dana mataimakin Gwamna (Duputy Governors Cup ) da Kofin maimmartaba Sarkin Kano (Emirs Cup ) da Kofin Aminu Kano wadanda aka daina duk da tasirin da suke dashi na bunkasa cigaban wasanni da hada kan matasa a tsakanin kananan hukumomi cewa yayi, kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo a shirye yake dan ganin andawo da irin wadannan wasanni la akari da irin tasirinsu wajen bunkasa wasani daga tushe,,

Kabiru Garo wanda ya yabawa kokarin gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da Kwamishinan Kananan Hukumomi Murtala Sule Garo dana Wasanni Kwamared Kabiru Ado Lakwaya bisa bada damar sanya gasar yace hakan zai kara zaburar da matasa kan hanyoyin bunkasa tare da zakulo matasa dake da basira dan tallatasu a fagen wasanni

A ranar lahadi Gwamnan jihar kano da mataimakin sa da kwamishinan kananan hukumomi dana wasanni zasu jagoranci kananan hukumomi 44 dan bude gasar a sabon filin wasa na Gwamna Ganduje Dake Garin Dawakin Kudu. Yay in da sauran wasannin aka rabasu zuwa kananan hukumomi 13 a matsayin shiyyoyin gasar da zaayi a matakin Gala.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *