Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

yanzu

Ministan lafiya na Spaniya ya ce bai jin magoya baya za su koma kallon tamaula a sitadiya a kasar, idan an fara kakar badi daga watan Satumba.

Gwamnati da hukumar wasannin Spaniya na fatan ‘yan kwallo za su ci gaba da zuwa sitadiya a badi, amma da fatan a rage yawansu, saboda hana yada cutar korona.

Wadan da za su buga wa Madrid wasa da Villareal a La Liga
Napoli ta rage farashin Koulibaly, Manchester City na son ɗauko Martinez
Sai dai barazanar yada cutar korona na kokarin kawo tsaikon barin magoya baya su koma shiga filayen wasanni domin marawa kungiyoyinsu baya.

“A gaskiya ban ga alamar za a koma kallon wasannin kwallon kafa a filaye ba a badi a dai wannan halin da muke ciki,” in ji ministan lafiya, Santiago Illa a hirar da ya yi da gidan radiyon Cadena Ser.

“Munga barazar annobar nan da illar da take yi, koda yake muna ta kokarin dakile ta, koda yake ba mu gama shawo kan komai ba, har yanzu banga dalilin da ‘yan kallo za su koma shiga sitadiya ba.

An ci gaba da gasar La Liga ba ‘yan kallo ta bana ranar 11 ga watan Yuni wacce aka dakatar a cikin watan Maris sabodo gudun yada cutar korona.

Ana kuma sa ran fara gasar La Liga ta badi ranar 12 ga watan Satumba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *