Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Fitaccen mawakin nan na Hausa kuma wanda yake fitowa a fina-finan Kannywood Ado Gwanja ya ce ya rera kusan wakoki 600 tun da ya soma sana’arsa ta waka kuma galibinsu da ka ya rera su.

Ado Gwanjo ya bayyana haka ne a hirarsa da BBC Hausa Instagram Live ranar Alhamis.

Da aka tambaye shi ko yin waka yana da wahala, sai ya ce “gaskiya babu abin da yake ba ni wahala” idan ya zo rera waka.

“Ina kiran mai kida na ce ‘buga min kida yanayi kaza, ko yanayi kaza’, sai a yi min kida sikeleton…ina cikin ji wakar za ta zo. Idan ta zo sai na ce ‘samo min furodusoshi,” a cewar Ado Gwanja.

Ado Gwanja ya ce cikin kusan waka dari shida da ya yi, wakoki ba su wuce biyu ba wadanda ya zauna ya rubuta saboda wasu sun ba shi shawarar yin hakan.

Ya ce wakar da ya soma yi ita ce Gawasa “kuma da na yi ta ni kadai aka bari na yi ta jin kaya ta. Na ji kayata ta ishe ni, na kuna mnata inda na ajiye ta”.

Wakokinsa da dama sun yi tashe musamman Kujerar Tsakar Gida, Asha Rawa, da Salon Kida.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *