
Gwamnatin Kano ta Najeriya ta tabbatar cewa, daya daga cikin shugabannin kwamitin yaki da cutar coronavirus na jihar, Farfesa Abdulrazak Garba Habib da wasu mambobin kwamitin uku su harbu da cutar.
Kwaminshin Lafiyar Jihar, Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ma’aikatarsa ta fitar.
Kwamishinan ya bukaci jama’a da su rika sanya tazara a yayin huldarsu da jama’a, sannan su kauce wa taruka da kuma zama a gida.
Tuni dayan shugaban kwamitin, wato Dr. Nasiru Gawuna da wasu karin mambobinsa suka killace kansu.
Daga cikin wadanda suka killace kansu har da Kwaminishin Lafiya, Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa da Sakataren Kwamitin, Dr. Imam Wada da Dr. Amina Abdullahi Ganduje da kuma kwamishinan Muhalli, Dr. Kabiru Ibrahim Getso.