Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.
Cibiyar killace masu corona

Hukumar dakile yaduwar cutuka a Najeriya ta ce ya zuwa karfe 9:30 na daren ranar Asabar, an samu karin mutum 13 da suka kamu da coronavirus a kasar.
Wannan na nufin adadin mutanen da suka kamu da cutar a kasar ya kai 318 jimilla.
Hukumar ta ce 11 daga cikin karin mutum 13 na Jihar Legas sai 1 a Delta da kuma daya a Kano – jiha ta baya-bayan nan da cutar ta bulla.
A cewar hukumar, cutar ta covid-19 ta bulla a jihohi 19 cikin 36 da ke kasar kuma kawo yanzu, an sallami mutum 70 daga asibiti sai guda 10 da suka riga mu gidan gaskiya.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *