Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Yayin da jama’a da dama ke ganin cutar korona ta kau a Najeriya da sauran kasashen Afirka, masana a fannin lafiya na gargadi a kan cewa har yanzu da sauran rina a kaba.

Hakan dai na zuwa ne yayin da ake ta bayyana fargaba game da yadda zagaye na biyu na annobar ke yin barazana a kasashen Turai da sauran wuraren da cutar ta fi kamari.

Dakta Nasiru Sani Gwarzo, kwararren likita ne a fannin yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, cutar korona lafawa ta yi ne a zukatan mutane.

”Ana samun raguwar masu kamuwa ne, amma har yanzu tana ci gaba da yin dauki dai-dai” in ji shi.

Dakta Nasiru Gwarzo, ya ce yanzu mutane sun ci gaba da gudanar da harkokinsu kamar ma babu wata annoba da ake fama da ita.

Kwararren likitan ya ce ” A yayin da a wasu a kasashen aka shiga zagaye na biyu na yaduwar cutar, a Afirka sai mu ce Alhamdulillah, saboda yanayin karuwar cutar ya fara lankwafowa”.

Ya ce, ba wai ba a samun karuwar wadanda ke kamuwa da cutar bane a Najeriya da ma sauran kasashen Afirka, saurin karuwarta ne ya ragu, kuma idan aka yi sa’a zata tafi.

Dakta Nasiru, ya ce kafin cutar ta tafin tana kuma ci gaba da dauki dai-dai, don haka sai an ci gaba da kiyayewa.

Kwararren likitan ya ce, abin da ya sa cutar ta fi saurin yaduwa a wasu kasashen musamman na nahiyar turai shi ne, mu a Afirka akwai masu karancin shekaru da dama.

Yayin da ake da tsofaffi wadanda shekarunsu ya haura saba’in a turai da yawa, mu a Afirka ba mu da masu wannan shekarun da yawa inji Dakta Gwarzo.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *