
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta ce zatacigaba da yakar dukkan wasu ayyuka da suka sabawa Shari’ar Musulunci a Jihar kano.
Babban Kwamandan Hukumar Dr. Harun Muhd Sani Ibn Sina, ya bayar da tabbacin hakan lokacin da yake jawabi ga wasu masu yawoce yawocen bara a tituna Jihar Kano su 24.
Ibn Sina, yace tun a shekarar 2004 gwamnatin Jihar Kano ta haramta barace barace a tituan Jihar nan manya da Kananan d bakin Danja, ya Kara da cewa la’akari da yadda cutar Corona ta addabi kassshen Duniya hakan yasa, gwamnatin Kano ta bayar da zama a gida dan dakile cutar.
Yace mabaratan su 24 an kamasune a Titin Audu Bako da Zoo road da mahadar Dan adundi wasu Kuma a wajen injin cirar Kudi ATM a cikin Birnin Kano.
Dr.Harun Ibn Sina, ya kuma baiwa al’ummar Jihar Kano tabbacin cewa tawagar Jami’an Hisbah zasu cigaba da gudanar aikinsu yadda ya kamata, ya Kuma yabawa alumamr Kano bisa yadda suka nuna hakuri bisa halin kulle da ake ciki, Inda ya bukace su dasu cigaba da Addu’a domin fita daga yanayin.
Da ya juya ga mabarata akan hanyoyin Kano, Babban Kwamandan yayi bayani da cewar Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya baiwa Hukumar Hisbah umarnin cigaba da fadakar da masu wata nakasa Yan asalin Jihar Kano, a Kuma koyawa musu sana’o’in dogaro da Kai domin rage adadin masu yawon barace barace.
A cikin sanarwar da Kakakin Hukumar Hisbah n Jihar Kano Lawan Ibrahim Fagge, ya sanayawa hannu, tace cikin mabaratan da aka Kama su 24 akwai mutum daya dake da shedar kammala Makarantar Primary uku masu sun gama Sakandire yayin da Mutane biyu suke da shedar Kammala karatun NCE, yace Gwamnan Kano Ganduje yace dukkan Yan Jihar Kano da suke da wata shedar karatu su Koma karamar Hukumar su za’a basu kulawar data dace.