Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

China ta buƙaci Indiya ta gaggauta janye dakarunta daga wani yankin da take iƙirarin nata ne a lardin Himalayan da ke kan iyakokin ƙasashen biyu.

Ministan tsaron China Wei Fenghe, ya shaida wa takwaransa na Indiya Rajnath Singh a Moscow cewa gwamnatin Delhi ce ke neman haifar da rikicin na kan iyaka.

Yanzu haka rahotanni sun ce ɓangarorin biyu sun ja daga inda suka girke dakarunsu a yankin Ladakh, bayan artabun da suka yi a watan Yuni inda aka kashe sojojin Indiya 20 da kuma sojojin China da ba a san adadinsu ba.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana rikicin na China da Indiya a matsayin al’amari marar daɗin ji, inda ya ce Washington ta shiga tsakani wajen magance rikici tsakanin ƙasashen biyu.

Ministan tsaron China ya ce ba za su haƙura da yankin da ake taƙaddama ba kamar yadda ya shaida wa takwaransa na Indiya.

Bbc ta ruwaito Kamfanin dillacin labaran China na Xinhua ya ambato Janar Wei, ministan tsaron China yana cewa akwai buƙatar su tattauna ƙeƙe da ƙeƙe da Ministan tsaron Indiya idan ana son samun fahimtar juna tsakaninsu.

Babu dai wani martani da ya fito daga ɓangaren Indiya game da tayin tattaunawar da China ta yi da ɗora laifin da Beijing ta yi wa Delhi game da rikicin.

Tun biyar ga watan Mayu China da Indiya masu ƙarfin tattalin arziki a yankin Asiya dakarunsu ke taƙalar juna.

An daɗe ƙasashen biyu na rikici kan iyaka, kuma sun sha hawa teburin tattaunawa tsakaninsu kan rikicin yankunan da suka yi iyaka da juna da suke jayayya akansu.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *