Daga-Salisu M. Jegus
Kungiyar Chelsea ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a FA Cup, bayan da ta doke Liverpool da ci 2-0 Talatar nan a Stamford Bridge.
Chelsea ta fara cin kwallo ta hannun Willians minti na 13 da fara wasan, yayin da Ross Barkley ya jefa ta biyu a zango na biyu
Wannan ne karo na biyu ajere da Liverpool tayi rashin nasara , bayan 3-0 da Watford ta yi nasara a kanta a gasar Premier a karshen mako.
Kungiyoyin biyu sun kara a bana sau biyu, inda suka yi 2-2 a European Super Cup ranar 14 ga watan Agustan 2019.
Sun kara haduwa a wasan Premier a Stamford Bridge ranar 22 ga watan Satumba, inda Liverpool ta yi nasara da ci 2-1.