Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Batun cinye kudin sayen makamai a karo na biyu run bayan da aka zargi was da irin wannan hali a gwamnatin Goodluck Jonathan a yanzu ma wannan batunne ya mamaye gwamnatin shugana Buhari abinda  Tsohon babban hafsan sojin Najeriya, Laftanan Janar Tukur Buratai, ya karyata rahoton cewa ya ci kudin da aka bada don sayan makamai lokacin da yake mulki.

Buratai wanda yayi murabus makonnin baya, ya bayyana hakan ta bakin lauyansa, Osuagwu Ugochukwu, ranar Juma’a.

 Mai baiwa shugaban kasar najeriya shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, ya yi zargin cewa wasu kudaden da aka baiwa tsaffin hafsoshin tsaro domin sayan makamai sun yi batan dabo.

A cewar Monguno, an bada kudaden ne domin sayen makamai don karfafa yakin yan ta’addan Boko Haram.

NSA Monguno ya yi wannan fallasa ne a hirar da yayi da BBC Hausa ranar Juma’a, 12 ga Maris.

Tsaffin hafososhin tsaron sune Janar Abayomi Olonisakin; Lt-Gen. Tukur Buratai, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas; Air Marshal Sadique Abubakar, dukka maus murabus.

Tuni Monguno ya ce anyi masa mumunan fassara ne ba haka yake nufi ba.

Buratai ya bayyana cewa ko sau guda Monguno bai ambaci sunansa ba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *