Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Bunkasa cigaban kananan masanaantu na daya daga cikin kudrin gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar kano hakanne ya sanya, a wani taron masu ruwa da tsaki na karamar hukumar Tarauni daya hadarda Hakimi, Dagatai, Masu Unguwanni da sauran Masu fada Aji a Karamar Hukumar Shugaban karamar hukumar Tarauni Muazzam Mainasara yasha alwashin bijiro da shirye shiryen da zasu bunkasa tattalin arzikin masu kananan sanaoi, inda ya bukacesu dasu baiwa hukumar Kididdiga ta kasa hadin kai a wani shiri da zata gudanar a yankin karamar hukumar,

Shugaban karamar hukumar wanda yace shirin wani matakine da zai tabbatar da hakikanin irin bukatu da masu sanaoin ke dasu yace hakanne zai baiwa gwamnati damar sanin abin da zata iyayi dan bunkasa cigaban su, inda ya kara da cewa shirin zai dauki kididdigar masu sanaoi komai kankantar su dake yankin,

Shi kuwa daraktan mulki na karamar hukumar ta Tarauni Abdullahi Mohd Gwarzo Matawallen Gwarzo cewa yayi zabin karamar hukumar a cikin kananan hukumomi da zaa gudanar da shirin tattara sunayen masu kananan sanaoi wata damace da zata bunkasa cigaban sanaoin nasu,

Da yake jawabin sa yayin taro Hakimin Tarauni Dangoribar Kano Malam Ado Kurawa yabawa yayi da yadda aka turo dan jihar kano da jagirantar shirin abin da hakimin ke cewa hakan ya kara sanya nutsuwa a zukatan mahukunta na karamar hukumar, inda yaja hankalin alummar yankin da suyi amfani da wannan damar da cin gajiyar shirin kana ya bukaci bada cikakken goyon baya daga dukkannin alumma musannan Dagatai, masu unguwanni, da limaman yankin dan ganin a cimma nssarar da akasa a gaba,

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *