- Fitaccen mawakin hausa a Najeriya wanda kuma yayi fice wajen wakokin siyasa Dauda Adamu Kahutu Rarara ya bara kan halin da Najeriya ke ciki na bukatar mawaka irinsa Dake fadin kasar dasu tashi tsaye wajen wayar da kan alummar kasar mahimmancin da kasar ke da shi ga kowa da kowa.
A wata hira da wakilin Express Radio Rarara yace Najeriya wata uwace da yayanta ya kamata susan darajarta Kuma su gane cewa babu wata uwa data fita Rarara ya kara da cewa baa sanin Najeriya uwace ta gari sai kaje wata kasar da niyyar zama da haka akwai bukatar mu rungumi zaman lafiya, kishin kasa da kaunar juna abin da Mawakin yace sune kadai mafita ga arzikin da Allah yayi mana na yawa da kabilu daban daban da ka iya zama abin alfahari matukar an hada kai kuma an so juna,
Daya juya kan irin rawar da mawaka zasu taka wajen hada kan alummar kasar cewa yayi wakokin hadin kai da mawaka kanyi a ko ina a fadin duniya na taka rawa wajen wayar da kan alumma da fadakar dasu, abin dake yin tasiri ga mabiyan da masoya mawakan da hakan ke sanya zuciya yin sanyi tare da sauya tunanin alumma,
Dayake amsa tambaya kan sabuwar gasar waka mai taken KASATA da yasa tsakanin mawaka daga kowane fanni dasuka hadar da Mawakan Gargajiya, Hip pop na Chamama wato Commedy da na fina finan Hausa da irin kyaututtukan dayasa ga wadanda suka shiga da kuma wadanda zasu lashe gasar Dauda Kahutu cewa yayi ya sa gasar ne dan mawakan su tunatar da yan Najeriya irin mahimmancin da kasar ke da ita ga yan kasar, da irin alhairai da arziki da kasar kedasu sabanin sauran kasashe da rashin zaman lafiya ke dai dai tawa,
Rarara wanda ya sanya motoci 4 ga wadanda sukayi na daya a kowane ajin mawaka da baburan adaidaita sahu ga duk na 2 a wancan rukuni da babaran haws ga na 3 kowane rukuni sai Naira 150:000 ga wadanda sukai na 4 zuwa na 10 sai Naira 100:000 ga sauran wadanda suka gwada sa’arsu da nufin nufin tallafa musu, yace ya shirya gasar ne dan zaburar da mawaka Dan tashi tsaye wajen sauke nauyin da yake Kansu inda “Ni. Kuma zan tallafa musu da abin da Allah ya horemin” inji Rararan.
Ko abaya mawakin ya saka makamanciyar wannan gasar waka ga sarakuna 5 na jihar kano,abin da ya Gaza yiwuwa sakamakon rasuwar maimartaba sarkin Rano da Kuma Annobar cutar corona data tsaida alamuran duniya cik, dayake Karin haske kan wakar shugaban kasa da yace yan kasa su biyashi yayi Dauda Kahutu Rarara cewa yayi alummar kasa sun amsa kiran da yayi sun biya SADAKIN WAKAR.
Dan gamin yadda hirar ta kasance kuje Express Radio Nigeria a (Facebook