Shugaban hukumar kwallon kwando ta kasa Ahmad Musa Kida yace bunkasa wasan kwallon kwando daga tushe ne zai kara samar da managartan yan wasan da Najeriya zatayi alfahari dasu,
A tattaunawarsa da wakilin Express Radio 90.3 kano kan amincewa da daukar nauyin gasar kwallon kwando ta matasa karo na farko da yayi a Jihar Kano Musa Kida yace laakari da irin yadda kungiyar dake shirya wasan tsakanin matasan jihar da yadda aka kammala wata gasa data bada shaawa a kwanananan ya sanyani dole in bada gudummawa tare da daukar nauyin gasar dan sake yinta cikin gaggawa duba da tasirin da wasan ke dashi tsakanin matasa,
Kida ya kara dacewa yin irin wannan gasa akai akai zai sake bada dama ga hukumar dake kula da wasan kwallon kwando ta kasa, jihohi da sauran masu ruwa da tsaki a wasan damar ganin sabbin yan wasan dake tasowa dan daga darajarsu,
Da yake amsa tambaya kan daukar nauyin gasar karo na farko Kida cewa yayi gasar da aka kammala kwananan a kano wata yar manuniyace na cewa jihar kano ta shirya samar da yan wasa da zasuyi gogayya da takwarorinsu a fadin kasa dama afrika baki daya,
A ranar litinin 16 ga watan Nuwambar nan ne za a fara gasar a filin wasan kwallon kwando na tsohuwar jamiar Bayero dake Jihar Kano.