Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wani matashi mai kamfanin Leda na BIB Poly bags ya bayyana dalilin dayasa kamfanin sa ya dauki nauyi daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafa da suke buga rukunin ajin matasa na kasa daga jihar kano

A tattaaunawarsa da wakilin Expressradiofm.com shugaban kamfanin Bello Ibrahim Bello BIB yace duba da irin halin da tattatalin arziki ke ciki na matsi ba kowa kan iya zuwa makaranta ba ko kafa kamfani ko wani abu da aza a iya amfani da kudi kai tsaye ba amma matashin nada basirar wasan kwallon kafa hakan ne ya sanyashi tunanin yadda zai taimaka musu,

Bello Ibrahim wanda ya taba yin wasan kwallon kafa yace na fuskanci a hayin su akwai yara matasa dake da basirar kwallon kafa kuma wasannan ya zama sana’a shiyasa na karbi wannan kungiya ta Mancity Dakata tare da sauya mata suna zuwa B.I.B Kuma karkashin kamfanina wanda kawo iyanzu kwalliya ta fara biyan kudin sabulu tunda sun fara fitar da dan wasa wanda yanzu ke bugawa a kungiyar Ifeayi Uba dake fafata wasa a rukunin kwararru na NPFL ta kasa,

Da yake karin haske kan yadda ya samu kansa da kalubalen dake gabansa BIB cewa yayi ” Idan da sabo na saba kalli inda kake a yanzu nan kamfanina ne kuma tun ina daure leda wanda shine aiki na farko da mutun yakeyi a kamfanin leda har gashi na kafa kamfani da maikata kuma komai na tafiya ba matsala to haka itama kungiyar kwallon kafar tana tafiya babu wata matsala”

Kan yadda alummar yankin da yan wasan suka karbi kungiyar Bello Ibrahim Bello cewa yayi kawo iyanzu kowa murna yake da fatan alheri kuma ina gode musu kwarai,

Dangane da yadda kungiyar zatayi gogayya da sauran kungiyoyin BIB cewa yayi dama daga cikin kungiyoyin dama mun saba wasa dasu tun a gasar cikin gida saboda haka ba zasu bamu tsoroba a shirye muke da kowace kungiya saida ina jan hankalin masu horar da yaran dasu kara hakuri wajen aikin su su gane yadda kalubalen yake wanda hakan zai taimaka mana wajen samun nasarar da muke bukata

Kanfanin BIB poly bag ace ya amsa kiran hukumomi na shiga harkokin wasanni dan bunkasa cigaban matasa dake da basira a fagen wasannin,

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *