Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta sanar da ranar kaddamar da ginin layin dogo daga jihar Kano zuwa Maradi a jamhurriyar Nijar, da kuma Kano zuwa Dutse a jihar Jigawa.
A cewar Ministan sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi, Buhari da kansa zai kaddamar da fara ginin ranar Talata 9 ga watan Febrairu, 2021.
Amaechi ya sanar da haka a shafinsa na Tuwita.
“Muna farin ciki sanar da kaddamar da ginin layin dogon Kano-Maradi, Kano-Dutse ranar Talata,” yace.
“Shugaban kasanmu, Muhammadu Buhari zai kaddamar. An fara aiki.”