Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Antoni janar na tarayya, Abubakar Malami sun ce kundin tsarin mulkin kasar nan ya baiwa shugaban kasa Buhari damar rike IGP Mohammed Adamu a kujerarsa iyakar son ransa.
Matsayarsu tana kunshe ne a wani martanin hadin guiwa da suka fitar sakamakon kalubalantarsu da Lauya Maxwell Opara yayi a kan karin wa’adin mulkin Adamu a lokacin da ya dace a ce yayi murabus.
A takardar da lauya Maimuna Shiru ta fitar a madadin Buhari da Malami, ta ce Adamu dan sanda ne mai aiki kuma zai iya mora daga karin wa’adin mulkinsa daga shugaban kasa Buhari.
Lauyan ta bayyana cewa, shekaru hudu na wa’adin mulkin IGP dake sashi na 7, sakin layi na 6 na dokokin ayyukan ‘yan sanda na 2020, zai kare ne a 2023 ko 2024.
Kamar yadda tace: “Idan aka kirga wa’adin mulkinsa daga 2020, lokacin da sabuwar dokar ayyukan ‘yan sandan ta fara aiki, wa’adin mulkinsa zai kare ne a 2024.”