A yau Juma’a 11 ga watan Disamba Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi gida garin Daura ta jihar Katsina domin kai ziyara.
Kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya sanar da cewa jirgin shugaban kasar mai saukar ungulu ta sauka a Katsina a ranar Juma’a don ziyarar mako daya.
– Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi gida Daura, jihar Katsina domin ziyara ta mako daya
– Jirgin shugaban kasa ta isa Katsina misalin karfe 4.45 na yammacin ranar Juma’a 11 ga watan Disambar 2020
– Gwamna Aminu Bello Masari, mataimakinsa, Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar na daga cikin tawagar da ta tarbi shugaban kasar
A yau Juma’a 11 ga watan Disamba Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi gida garin Daura ta jihar Katsina domin kai ziyara.
Kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya sanar da cewa jirgin shugaban kasar mai saukar ungulu ta sauka a Katsina a ranar Juma’a don ziyarar mako daya.
DUBA WANNAN: Zahra Buhari ta taya mijinta murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kalaman soyayya
Jirgin da ke dauke da shugaban kasar ya dira a filin tashin jirage na Musa Umaru Yaradua da ke Katsina misalin karfe 4.45 na yammacin ranar Juma’a inda gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina da mataimakinsa da wasu shugabannin hukumomi suka tarbe shi.
Har wa yau cikin tawagar da ta tarbi shugaban kasar akwai mai marataba sarkin Daura Alhaji Umar Faruk Umar da sauran ‘yan majalisun masarautar jihar tare da kayatattun dawakai da fadawa
Jim kadan bayan saukarsa, Sarkin Daura ya bawa shugaban kasa kyuatar doki da takobi da aka kawata shi a matsayinsa na Bayajiddan Daura.