Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a karon farko ya nuna cewa yana cike da damuwa kan halin tsaron a wasu sassan ƙasar ke ciki da kuma ƙoƙarin shawo kansu.
Ya ce lallai akwai buƙatar ganin dakarun Najeriya su ƙara tashi haiƙan a ƙoƙarin kare ƙasar daga matsalar tsaro da take ciki.
A wata hira da ba kasafai yake yi ba, Shugaba Buhari ya bayyana halin da ake ciki a yankin arewa maso yamma da kuma arewa maso tsakiyar ƙasar a matsayin abin tayar da hankali matuka.
“Ina da yaƙinin cewa sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro daga rahotannin da nake samu, ina tunanin za su iya ƙara tashi tsaye,” in ji kamfanin dillancin labarai na AFP
Abin da ke faruwa ɗin nan jefi-jefi, ka ji an bindige nan, an kai hari nan. A ƙauye, an sace mutane, an sace dabbobi, idan ba ƙarshensa aka gani ba. Ai ba za a ce an samu nasara ba, cewar Malam Garba Shehu mai magana da yawunsa.
Bbc tace ya ambato Buhari na cewa rahotannin da yake samu duk samu sun nuna buƙatar sake jajircewa, duk da irin halin da gwamnatinsa ta samu Najeriya.
Buhari ya hau mulki ne shekara biyar da ta wuce, da alkawarin cewa zai murkushe ‘yan Boko Haram cikin dan kankanin lokaci, amma kuma har yanzu masu iƙirarin jihadin na ci gaba da kai hare-hare musamman a yankin arewa maso gabashin kasar.
Bayan su kuma sai ga wasu matsalolin tsaron sun kunno kai suna kuma ƙara ƙamari, kamar rikicin ƙabilanci da na ‘yan fashin daji masu satar mutane don neman kuɗin fansa da kuma awon gaba da shanu, yawanci a arewacin kasar.
A cikin ‘yan kwanakin nan ne dai Majalisar Dattijan Najeriyar ta amince da wani ƙuduri da ke neman shugabannin rundunonin sojin ƙasar da su yi murabus, ko kuma a kore su sakamakon kara taɓarɓarewar matsalar tsaron