Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da layin dogo na zamani daga Lagos zuwa Ibadan, shekaru 3 bayan kaddamar da aikin don saukaka sufurin jiragen kasa a kasar, aikin da ya lashe tsabar kudi sama da Dala biliyan guda da rabi.
Katafaren kamfanin gine-ginen na China ya gudanar da aikin wanda aka samu tsaikon kammala shi sakamakon annobar korona wadda ta haifar da matsala a kasashen duniya.
A tashin farko jirgin zai dinga zuwa Ibadan ne yana komawa kowacce rana sau guda, kafin daga bisani a fadada aikinsa, kamar yadda hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta sanar.
A litinin jirgin ya bar Ibadan da misalin karfe 8 na Safiya, kuma ya isa Lagos da misalin karfe 10, yayin da ya bar Lagos da misalin karfe 4 na yamma zuwa Ibadan kamar yadda aka shirya.
Shugaban hukumar kula da jiragen Jerry Oche ya ce daga watan Janairu mai zuwa, jirgin zai dinga zirga-zirga sau 16 kowacce rana tsakanin biranen biyu.
Shi dai wannan aiki tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya fara aikin sa, amma sai aka yi watsi da shi, kafin daga bisani shugaba Muhammadu Buhari mai ci ya farfado da shi a shekarar 2017 wanda ya fara aiki yau.
Shugaba Buhari ya jaddada aniyar sa na hade wasu daga cikin manyan biranen kasar da hanyar jiragen kasa domin inganta harkar sufuri a cikin kasar.
A shekarar 2018 gwamnatin Buhari ta kaddamar da sufurin jiragen kasa da gwamnatin Goodluck Jonathan ta fara tsakanin Kaduna zuwa Abuja wanda ya taimaka sosai wajen rage matsalar sufuri da kuma kaucewa barayin da suka addabi jama’ar yankin.