Buhari ya amince da nada Mista Aghughu Adolphus a matsayin babban auditan tarayya
Shugaban ya aike da takardar nadin ga majalisar dattawa domin tantancewa
Adolphus, dan asalin jihar Edo shine ke rike da mukamin tin bayan ritayar Anthony Ayine biyo bayan cikar sa shekara 60
Shugaba Kasa Muhammadu Buhari ya nada Mista Aghughu Adolphus a matsayin babban mai binciken kudaden na gwamnatin tarayya, AGF, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Shugaban ya mika takardar nadin ga shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan kamar yadda sashe na 86 (1) na kundin tsarin mulki ya tanada.
A wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja, mataimaki na musamman ga shugaba Buhari kan harkokin majalisa, Sen. Babajide Omoworare ya ce Aghughu ne ke rike mukumin tun baya ritiyar Mr. Anthony Mkpe Ayine daga aiki bayan cikarsa shekara 60, ranar 25 ga Oktobar 2020.