Tsohon gwanan jihar Imo, Rochas Okorocha ya ce har yanzu yana nan a cikin jam’iyyar APC babu gudu ba ja da baya,
A makon jiya ne toshon gwamnan wanda yanzu sanata ne a jam’iyyar APC ya sanar da cewa suna shirin kafa sabuwar jam’iyyar gabanin zaben 2023
A cewar Rochas, wasu ‘yan kanzagi sun shigo APc tare da kankane komai, kuma shugaba Buhari bai san wainar da ake toya ba a jam’iyyar
A ranar Asabar ne aka ji tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, na jaddada cewa har yanzu yana nan cikin jam’iyyarsa ta APC duk kuwa da rikicin da ya dabaibaye ta har su ke yunkurin kafa sabuwar jam’iyya.
Okorocha ya yi wannan furuci ne loƙacin da ya ke yiwa kwamatin riƙo na jam’iyya jawabi a Owerri, babban birnin jihar Imo, inda ya bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bai san wainar da ake soya ba a cikin APC.
Okorocha, wanda ke wakiltar mazaɓar Imo ta yamma a zauren majalisar dattijai, ya nuna takaicinsa kan yadda wasu da ba asalin ƴan jam’iyyar ba suke neman kankane komai, sai yadda suka yi da komai.
Tsohon gwamnan, ya musanta raɗe-raɗin da ake na cewa yana shirin barin jam’iyyar sakamakon rikicin da ya dabaibayeta a jiharsa ta Imo, kamar yadda Premium Times ta rawaito.