Wasu masana a fadin kasar nan sun bayyana cewa bude iyakokin tudun Najeriya da gwamnatin tarayya ta bada umarni ayi, yana da tasiri ga tattali.
Jaridar Sahara Reporters ta ce wadannan masana harkar tattalin arziki sun ce bude iyakokin da aka yi, yana da amfani da illa ga mutanen Najeriya.
A hirar da jaridar ta rika yi da wasu masana da-dama, sun bayyana wasu daga tasirin wannan mataki a zamantakewa da halin tattalin da ake ciki.
1. Shigo da kaya
Farfesa Akpan Ekpo yace da bude iyakokin da aka yi a makon nan, kayan kasashen ketare za su shigo Najeriya inda za su kashe kasuwar kayan cikin gida.
2. Fasa-kaurin man fetur
A cewar Akpan Ekpo, da wannan mataki da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka, za a dawo da shiga da fetur zuwa kasashen ketare ta barayin hanyoyi.
3. Farashin kaya a kasuwa
Masanin tattalin arzikin yace kaya za su rika shiga su na fita sosai wanda hakan zai yi dalilin raguwar farashi da tsadar kaya da ake fama shi a Najeriya.
Farfesa Segun Ajibola na jami’ar Babcock, jihar Osun, yace bude iyakokin da aka yi zai taimaka wajen karya farashin kayan masarufi na wani gajeren lokaci.
4. Kashe kamfanonin gida
A cewar Farfesa Leo Ukpong, za a kashe ‘yan kasuwan gida tun da gwamnati ta bude iyakoki, kuma an gaza kawo manufofin da za su tada kamfanonin kasa.