Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Athletic Bilbao tayi galaba a kan Barcelona a wasan kofin Spanish Super Cup

Lionel Messi ya samu jan katinsa na farko ya na mai dauke da rigar Barcelona

Messi ya taba samun jan kati sau biyu, amma lokacin da yake bugawa kasarsa

Tauraro Lionel Messi ya buga wa kungiyar Barcelona wasanni 750, amma sai yanzu ne ya samu jan kati a wasan kungiyar ta sa da Athletic Bilbao.

Lionel Messi ya samu jan katinsa na farko a cikin rigar Barcelona ne a wasan cin kofin Spanish Super Cup wanda aka buga a ranar Lahadi, 17 ga watan Junairu.

Goal.com ta ce da farko Alkalin wasa, Gil Manzano, bai ga danyen aikin da Messi ya yiba, sai daga baya ya duba bidiyon VAR, ya ba ‘dan wasan jan kati nan-take.

Wannan wasa bai yi wa Barcelona dadi ba, ta sha kashi 2 – 3 a hannun kungiyar ta Athletic Bilbao.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *