Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.
..

Ɗan takarar Jam’iyyar Democrat a zaɓen Amurka Joe Biden ya lashe zaɓen Amurka inda a halin yanzu ya samu kur’iu 273, abokin karawarsa kuma Donald Trump na da 214.

A yadda tsarin zaɓen Amurka yake, duk wanda ya fara samun ƙuri’un wakilai na musamman da ke zaɓe har 270, shi ya samu nasara a zaɓen ƙasar.

A nasarar da Mista Biden ya samu a jihar Pennsylvania, hakan na nufin ya ci zaɓen Amurka domin kuwa ya samu ƙarin ƙuri’u 20 daga wakilai na musamman masu zaɓe, wanda hakan ya sa ya samu ƙuri’u 273, ya ma wuce 270 ɗin da ake buƙata.

Sai dai da alamu Trump ɗin na da niyyar maka Mista Biden ɗin ƙara a kotu biyo bayan wasu zarge-zargen da Trump ɗin ya fara tun a ranar zaɓen inda yake zargin an yi maguɗi, zargin da har yazu bai kawo gamsashiyyar hujja a kai ba.

Bbc ta ruwaito cewa a ƙarƙashin tsarin zaɓen Amurka, masu zaɓe suna zaɓar wakilai na musamman waɗanda ke haɗuwa makonni kaɗan su kaɗa ƙuri’a domin tantance wanda zai zama shugaban ƙasa.

Ko wane wakilin zaɓe na musamman na da ƙuri’a ɗaya, kuma adadin wakilan zaɓe da kowace jiha ke da shi ya danganta ne da adadin yawan jama’ar jihar.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *