Dan takarar jam’iyyar Democrat Joe Biden ya kara kusantar yiwuwar samun nasarar lashe zaben shugaban Amurka yayin da alkaluman da aka sabunta suka nuna ya tserewa Shugaba Donald Trump a jihohin Georgia da Pennsylvania.
Voa ta ruwaito Yanzu haka Biden na gaba a yawan kuri’un da aka kada a duk fadin kasar da kuma yawan kuri’un kwalejin masu zabe da kuri’u 253 yayin da Biden ke da 214 – inda ake bukatar dan takara ya samu rinjaye da kuri’a 270 kafin ya samu wa’adin mulki na tsawon shekara hudu a matsayin shugabvan kasa.
Har yanzu ana ci gaba da kidaya kuri’u a wasu jihohi hudu wadanda su za su tantance wanda ya yi nasara – wato jihohin Arizona da Nevada, wadanda Biden ke gaba
Da safiyar ranar Juma’a Biden ya wuce Trump da yawan kuri’u yayin da ya yi masa fintinkau da kuri’a 917 a Georgia.
Amurka na amfani ne da tsarin zaben “Electoral College,” wanda ke ba dan takara dama ya samu, idan ya lashe kuri’un kowacce jiha – ban da jihohin Maine da Nebraska.
Kuri’un na kwalejin masu zabe ko “Electoral College,” ana raba su ne bisa iya adadin al’umar kowacce jiha.
Ba tare da wata hujja ba, a ranar Alhamis shugaba Trump ya zargi ‘yan Democrat da yunkurin tafka magudi domin su hana shi samun wa’adi na biyu.
“Wannan al’amari ne na yunkurin sace wannan zabe, suna so su tafka magudi,” in ji Trump yayin wani taron manema labarai.
Sabanin hakan, a wannan rana, Biden ya yi kiran a kara hakuri yayin da jihohi ke ci gaba da tattara alkaluman zaben, wanda sama da mutum miliyan 150 suka kada kuri’unsu a wannan shekara.
“Wajibi ne a kirga kowacce kuri’a. Kuma abin da za mu tabbata ana ci gaba da yi kenan. Kuma haka ya kamata a yi. Shi tsarin dimokradiyya, haka yake zuwa da rudani a wasu lokuta.” Biden ya ce.