
ASALIN HOTON,GETTY IMAGES
Dan takarar jam’iyyar Democrat a zaben Amurka Joe Biden ya zabi Sanata Kamala Harris a matsayin mataimakiyarsa a zaben kasar da za a yi a watan Nuwamba. Ita ce mace bakar fata ta farko da aka tsayar takara a wannan matsayi a tarihin Amurka.
‘Yar majalisar dattawan da ke wakiltar jihar California ta taba neman a tsayar da ita takarar shugabancin kasar, kuma ‘yar asalin India da Jamaica ce.
Ita tsohuwar babbar mai shari’a a jihar California inda ta dade tana kira a yi garambawul ga dokokin ‘yan sanda a yayin da ake zarginsu da nuna wariyar launin fata.
Mr Biden zai fafata da Shugaba Donald Trump a zaben da za a gudanar ranar 3 ga watan Nuwamba.
Mataimakin shugaban kasa Mike Pence shi ne dan takarar mukamin na jam’iyyar Republican.
bbc tace Mr Biden ya wallafa sakon Twitter da ke cewa “abin alfahari ne a gare ni” da na zabi Ms Harris a matsayin mataimakiyata.