Hukumomin Saudiyya sun sanar da sake bude masallacin Al-Haram na Ka’abah – wuri mafi tsarki da daraja ga musulmi bayan an rufe shi na wata bakwai.
Kafofin watsa labarai na Saudiyya, kamar tashar talabijin ta Saudi Television da shafin Tiwita na Haramain Sharafain, sun ruwaito cewa an kyale ‘yan kasar har da mazauna birnin Makkah shiga harabar masallacin Ka’abah domin yin salloli biyar na farali da ma sauran ibadu.
An dai rufe masallacin ne saboda annobar korona wadda har ta shafi ayyukan ibada kamar aikin Hajji da na Umrah.
Shafin Tiwita na Haramain Sharifain ya wallafa wani takaitaccen bayani, wanda a ciki yake sanar da duniya cewa:
Bbc taruwaito cewa Nan da sa’o’i kalilan… za a bude kofofin Masjid al Haram ga kowa domin gabatar da ibadun khamsat salawat bayan hanin da aka yi na wata bakwai.” Sai dai sanarwar ta ce akwai sharuddan da ake bkatar masu shiga masallacin su tabbatar sun cika gabanin shiga harabar masallacin. Wannan ya hada da sanya takunkumi.