Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmed Lawan ya kara jaddada muhimancin fitowa fili a yi wa ‘yan kasa bayanin kan yadda daukan matasan zai gudana domin a kaucewa yawan zargi da ake yi na yin almundahana a shirin.
Ahmed Lawan ya ce ba a taba Gwamnatin da ta yi irin wannan yunkuri na ba matasa aiki irin wannan Gwamnatin ba, kuma Majalisar ita ce ta amince da kasafin kudi Naira biliyan 52 domin a gudanar da aikin.
Shugaban Majalisar ya ce lallai sai Majalisa ta gamsu da yadda shirin zai gudana kafin a dawo da shi.
Abin lura shi ne cewa tun da aka fara batun daukan aikin aka yi zargin cewa an ba ‘yan majalisar, da Gwamnoni kaso 15 cikin 100 na guraben daukan aikin.
Sai dai Kwararre a fanin Kundin Tsarin Mulkin kasa Barrista Mainasara Ibrahim ya fadawa voa ce Majalisa ba ta da hurumin dakatar da wannan shiri duk da cewa su ne masu yin dokoki sannan kuma su ne masu sa idanu a yadda bangaren zartaswa ke gudanar da ayyukanta yana mai cewa a nan hurumin su ya tsaya.
Shi ma mai nazari a al’aumuran yau da kullum Alhassan Dantata Mahmood ya ce baiwa ‘yan Majalisar guraben aiki abu ne da ake yi a matsayin na alfarma amma babu dokar da ta ba da damar a basu.
Wannan dai shi ne karo na farko da yake nuna fito na fito tsakanin mamajalisa da bangaren zartasws