‘Yan Najeriya da dama sun nuna fushinsu kan zargin bankin Access da haɗa kai da Babban Bankin Najeriya wato CBN wurin toshe asusun ajiyar wasu da suke kan gaba a zanga-zangar EndSars.
BBC taruwaito cewa ‘Yan ƙasar da dama ne a shafin Twitter suka fito suna kira da a ƙaurace wa bankin da kira da duk wani mai kishin ƙasar da ya rufe asusun ajiyarsa da ke bankin.
Sai dai abin mamaki shi ne yadda mutane suka rinƙa ɗaukar hotunan takardar da suka cike a bankin na rufe asusun ajiyarsu, inda suke wallafawa a shafinsu na Twitter, wanda hakan ke ƙara rura wutar.
Ganin yadda yake shan suka a shafin na Twtter da sauran shafukan sada zumunta, Access ya fito domin kare kansa daga zarge-zargen da ake yi masa, sai dai wasu na cewa duk da bankin ya kare kansa, abin da ya yi tamkar ihu ne bayan hari.