Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Hukumomin Saudiyya sun ce ba za a gudanar da jam’in Sallar Asham ko Taraweeh ba a Makkah da Madina idan har ba a kawo karshen annobar coronavirus ba.
Ministan ma’aikatar kula da harkokin lamurran addini a Saudiyya Dr. Abdul Latif Al Sheikh ne ya sanar da haka, a wata hira da kafar MBC da aka watsa a ranar Lahadi, kamar yadda jaridun kasar suka ruwaito.
Jaridar Saudi Gazette ta ambato ministan yana cewa: “dakatar da salloli biyar na farilla a masallaci ya fi dakatar da Sallar Taraweeh girma. Muna rokon Allah ya karbi ibadarmu ta Taraweeh a masallaci, ko a gida, wanda muke tunanin ya fi dacewa domin lafiyar al’umma.”
Ya kuma yi addu’a tare da fatan kawo karshen wannan annoba da wuri. Ya kuma roki Allah ya karbi ibadar musulmi ta Sallar Asham da za su gudanar a Masallaci ko gida.
Kazalika ya ce; “Sallar Jana’iza ma a makabarta za a dinga yin ta. Kuma kar mutane su taru sosai. Sauran mutane za su iya yi wa mamacin Sallar Jana’iza daga gidajensu.”

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *