Yayin da alumomi da dama keta kace nace kan batun dage mukabalar da ake sa ran yi tsakanin malamam jihar kano da malam
Abduljabar da aka shiya a ranar lahadi sai gashi Gwamnatin Kano ta yi na’am da hukuncin kotu na hana mukabala tsakanin malaman jihar da Sheikh Nasiru Kabara
Kotu ta yanke wannan hukunci ne a ranar Juma’a, 5 ga watan Maris
Sai dai lauyan Kabara ya ce su a nasu bangaren zama na nan don babu inda kotu ta fadi hana mukabalar kai tsaye
Gwamnatin Kano ta yi amanna da hukuncin kotun majistare ta jihar wacce ta hana yin mukabala tsakanin malaman jihar da Sheikh Nasiru Kabara.
A ranar Juma’a, 5 ga watan Maris ne kotun ta zartar da wannan hukunci, ana saura kwana biyu kafin gudanar da mukabalar da mutane ke ta zuba ido.
Hukuncin kotun ya nemi a tsaya kan hukuncin da kotu ta zartar tun a ranar 8 ga watan Fabrairu, wanda ya hada da haramtawa Sheikh Kabara yin wa’azi a jihar.