Ministan ma’aikatar da ke kula da yankin Niger-Delta Godswill Akpabio ya tura wa majalisar wakilan Najeriya wasika bayan da ta ba shi wa’adin kwana biyu domin ya wallafa sunayen ‘yan majalisar da ya yi zargin cewa suna cin fiye da kashi 60 cikin 100 na kwantaragin da hukumar raya yakin Niger-Delta ke bayarwa.
Bbc ta ruwaito cewa Jinkirin da aka samu gabanin isar wasikar ya sa kakakin majalisar ya umurci Akawun majalisar da ya bi matakan da suka dace don gurfanar da ministan a gaban kuliya, bisa tuhumarsa da yin karya da bata sunan ‘yan majalisar.
Hon Kabiru Rurum, dan kwamitin majalisar ne da ke gudanar da bincike a kan zargin badakalar kudi a hukumar NDDCn, kuma yana zauren majalisar lokacin da kakakin ya karanta wasikar wadda ya ce tana cike da waskiya.
Wani dan jinkiri da aka samu gabannin isar wasikar ta sa kakakin majalisar Femi Gbajabiamila ya umarci Akawun majalisar da ya fara tattara lauyoyin majalisar domin su bi duk matakan da suka dace wajen gurfanar da ministan a gaban shari’a domin tuhumarsa da shirga karya, tare da shafa wa ‘yan majalisa kashin-kaji.
Ya yi zargin cewa ministan da wasu jami’an gwamnati sukan yi irin wadannan karairayin ne da nufin dauke hankalin jama’a daga gaskiyar lamari, tare da shiriritar da binciken da ake yi.
Don haka yace majalisar ba za ta raga wa mai yin irin wannan ba, komai girman mukaminsa a ciki da wajen gwamnati.
Sai dai abin tambaya shi ne ko mene ne takamaiman matsayin majalisar yanzu?