An bukaci yan Najeriya da su daina yin kalaman da ka iya haddasa tsoro da fusata
Kungiyar dattawan Arewa ta hannun Dr. Hakeem Baba-Ahmed ce tayi wannan kiran
A cewar kungiyar, wadanda suka haddasa hakan sun kasance makirai kuma masu mugun nufi
Wasu masu mugun nufi na yin furucin da ka iya tarwatsa kasar a cewar kungiyar dattawan arewa (NEF).
Musamman, kungiyar ta ce mutanen na yin zafafan kalamai a karkashin fakewa da addini.
Ta ce wadannan kalamai na iya haddasa fushi da tsoro a tsakanin al’umma
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga daraktan labarai na kungiyar, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, jaridar This Day ta ruwaito.
Kungiyar ta kuma yi kira ga yan Najeriya a kan su yi hankali da makiran mutane masu haddasa rudani.
“Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta damu a kan kalamai masu sanya damuwa da wasu ke yi ta hanyar fakewa da addini wanda ke haifar da fushi da tsoro a cikin al’umma.”
Da yake ci gaba da magana, ya bukaci gwamnati da ta duba dalilan da za a iya amfani da su wajen haddasa rikicin addini a kasar sannan ta magance su yadda ya kamata.
Ya kara da cewa Musulmai da Kiristoci basu da wasu dalilai na fada da junansu.