
Shugaban Hukumar Karota na jihar Kano Dr. Baffa Babba Dan’agundi Ya Bayyana irin matakan da gwamnatin Kano ta dauka game da rufe Iyakokin shigowa jihar Kano, Saboda kaucewa annobar Covid 19.
Daga ranar Juma’a 27-03-2020 da misalin Karfe 12:00am
ABUBUWAN DA AKA AMINCE A SHIGO DASU
- Kayan Abinci
- Magani
- Textiles, Atamfa, shadda, yaddi da dukkan kayan sawa.
- Kayan amfanin Masana’antu
- Dieasel, Fetir, Gas.
- Kayan marmari (Fruits)
WADANDA AKA YARDA DASU SU SHIGO DA KAYAN
- Direban Mota da Kwandasta kadai aka yadda su shigo.
MATAKAN DA AKA DAUKA DAN SAMIN NASARAR WANNAN AIKIN NA HANA SHIGOWA DAGA MAKOTA TA SAMA DATA KASA
- NAVY, AIR FORCE, Jami’an ‘YAN SANDA,(POLICE) CUSTOMS, DSS, KAROTA, HISBAH ROAD SAFETY, PRISON SERVICE, IMMAGARATION, JAMI’AN LAFIYA DA NDLE.
Sannan Kuma sai Ma’aikatan Lafiya sun duba Direban da yaran Motar tasa da Kuma duba ingancin Kayan da suka dauko, da lafiyarsu.
Kamar yadda Kowa yasani hanyoyin Shiga Kano hanyoyi( 8) ne Kuma zasu zama a rufe.
Sannan an hana shigowa da fita daga Jahar Kano.
Ba’a hana kasuwanci ba, dayin Ibada amma mutane su kiyaye da shawarwarin da ma’aikatan Lafiya suke bayarwa na amfani da takunkumin Hanci, da wanke hannu da sanitizer, sabulu da duk abinda zaisa tsaftar hannu.
Wannan Bayani ne a madadin Kwamitin Tsaro na jahar Kano bisa Umarnin mai Girma Gwamnan jihar Kano
Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Daga bakin Shugaban Hukumar Karota
Hon. Baffa Babba Dan’agundi
kuma dan kwamitin tsaro na jihar kano.
Sauran bayani za’aji cikakken bayani a Gidajen Radion da muke dasu a jihar Kano
Ayuba Jarimi SSA
SOCIAL MEDIA MD KAROTA
27/03/2020.