Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamnatin Najeriya ta ce ta gano masu yunkurin durkusar da kasar da ke fakewa da sunan zanga zangar adawa da cin zarafin ‘yan sanda kuma ba za ta bari su cimma biyan bukatarsu ba. Ministan yada labaran Najeriyar Lai Muhammed ke sanar da hakan lokacin da ya ke amsa tambayoyi a gidan talabijin game da yadda zanga zangar ke fadada a manyan birane.

Lai Muhammed ya ce yunkurin kashe Gwamnan Jihar Osun Adegboyega Oyetola lokacin da ya ke jawabi ga masu zanga zangar wata shaida ce da ke tabbatar da wannan zargin cewar wasu mutane daban sun karbe zanga zangar domin biyan bukatun kan su.

Ministan ya ce suna da masaniyar cewar zanga zanga na daga cikin hanyoyin dimokuradiya da mutane ke amfani da ita wajen nuna rashin amincewar su, abinda ya sa gwamnati bata dauki mataki kan masu zanga zangar ba a cikin kwanaki 11 da suka gabata.

Muhammed yace babu wata gwamnati a duniya da zata rungume hannayen ta tana ganin bata gari na amfani da irin wannan hali domin jefa kasa cikin mummunar yanayi.

Ministan yace abinda Najeriya ke fuskanta yau ba masu zanga zangar adwa da cin zarafin Yan Sanda bane, saboda haka ya dace kowanne dan kas aya bude idanun sa domin ganin halin da ake ciki, ganin yadda masu zanga zangar suka tare manyan hanyoyi, suka hana ma’aikata zuwa guraben ayyukan su da kuma hana jama’a gudanar da harkokin yau da kullum.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *