Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamnan jihar Ondo, Mista Rotimi Akeredolu ya ce makiyaya daga kasashen ketare da ke zaune a dazukan jihar ne suka aikata laifuka da kai hare hare, The Punch ta ruwaito.

Akeredolu ya ce da dama cikin makiyayan da suka zo daga kasashen ketaren zaman dindindin suke yi a dazukan gwamnatin jihar kafin a bada umurin korarsu.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin ziyarar ban girma da a ofishinsa da shugaban yankin na Hukumar Shige da Fice na Kasa, Dora Amahian, da ke wakiltan jihohin Oyo, Ondo, Osun da Ekiti ta kai masa.

Akeredolu, wanda ya bukaci jami’an hukumar su kara jajircewa domin kiyayye iyakokin jihar ya ce adadin bakin da ke shigowa jihar daga kasashen waje abin duba wa ne.

“Zai yi wu Fulani ne amma ba yan Nigeria bane. Ina ganin ya kamata a rika hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro. Hakan zai inganta aiki da samun sakamako. Ku hada kai da hukumar tsaro kamar Amotekun,” a cewar gwamnan cikin jawabinsa.

Tunda farko, Misis Dora Amahian ta mika godiyarta ga gwamnan saboda kyakyawar alakar da ke tsakaninsa da hukumar ta Immigration inda ta ce himmarsa na samar da mulki na gari da romon demokradiyya ne ke samar da zaman lafiya a jihar.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *