Mutane da dama sun tsere daga gidajen su alokacin wasu yan kungiyar Boko Haram suka kai hari wani a jihar Borno ranar Juma’a.
Maharan sun shiga garin Dikwa ne misalin karfe 6:05 na dare, inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi amma Sojoji suka shiga artabu da su.
Sai da aka kwashe awanni ana musayar wuta.
“Sun shigo Dikwa misalin karfe 6:05 na yamma, sun harbi ko ina,” wani mai idon shaida ya bayyanawa Daily Trust.
“Harin ya zo wa soji da bazata. Dubunnan mutanenmu na daukar mafaka yanzu a cikin daji.”
Wannan hari ya biyo bayan harin da yan ta’addan suka kai Marte, inda suka kori Soji daga barikinsu.