Mummunan Labari ga Kocin Arsenal Mikel Arteta na tafiyar Dan wasan bayanda Shkodran Mustafi yaji rauni Wanda da zuwa zai shafi Dan wasan har zuwa wasan karshe na gasar FA Cup da zasu kara da abokiyar hammaya Chelsea,
An tabbatar da raunin da dan wasan ya samu zai Hana shi buga wasan da Arsenal zata Kara da Watford a wasan karshe a gasar Firimiya mako na 38 tareda wasan karshe na FA Cup Wanda zaayi a filin wasa na wembley,
Shkodran Mustafi Wanda ya buga wasanni 27 a wannan kakar inda akafara dashi a farko a wasanni 25 wasanni biyu ne kawai yasamu Shiga a matsayin canji
Kwantaragin dan wasan zai kare a karshen wannan kakar wasan daza mu Shiga ta 2020/21 Wanda ana tunanin Dan wasan dawuya ya cigaba da wakiltar Arsenal.